Rasha:Jirgin da ya yi hadari ya tarwatse ne a sama

Tarkacen jirgin Rasha da ya fadi a yankin Sinai a Masar Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Tarkacen jirgin Rasha da ya fadi a yankin Sinai a Masar

Shugaban hukumar sufurin jiragen saman Rasha yace jirgin fasinjar da ya yi hadari a Sinai a jiya Asabar wanda kuma ya hallaka dukkan fasinjoji 224 dake cikin sa ya tarwatse ne tun daga sama.

Aleksander Neradko ya shaidawa manema labarai cewa tarkacen jirgin sun warwatsu a wurare da dama.

"yace wurin da hadarin ya faru yana da girma fiye da fadin kilomita ashirin. Dukkan alamu sun nuna cewa jirgin ya tarwatse ne tun daga sama."

Ana zaman makoki yau a ko ina a fadin kasar Rasha.

Rasha da Masar sun musanta ikrarin kungiyar ISIS cewa ita ce ta harbo jirgin. S