Jam'iyyar PNDS ta ba wa Issoufou takara

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mahamadou Issoufou yana neman mulkin kasar karo na biyu

Magoya bayan jam'iyya mai mulki ta PNDS tarraya na jihar Maradi a Jmahuriyyar Niger sun amince da tsayar da shugaban Kasar mai-ci, Mahamadou Issoufou a matsayin dan takarar jam'iyar, a zaben 2016.

Sun dai bayyana hakan ne ranar Asabar yayin wani gangamin da suka kira karkashin jagoracin shugaban jam'iyyar reshen Maradi, Kalla Hankurau.

Taron ya tara manyan 'yan siyasa da sauran masu fada aji a siyasa jahar.

Magoya bayan dai sun ce gamsuwar da suka yi da irin ayyukan alkairin da Isooufou ya fara shi yasa suke son sake ba shi wata damar domin ci gaba da ayyukan.

A farkon shekarar 2016 ne dai jamhuriyar ta Niger za ta gudanar da babban zaben kasar.