Mayakan ISIS sun kwace wani gari a Syria

Hakkin mallakar hoto Albaraka News via AP

Kungiyar sa ido da kare hakkin bil Adama a Syria ta ce yan bindigar sun kama garin Maheen da ke yammacin kasar bayan da suka kori sojojin gwamnati.

An yi mummunan fada a wajen gari kusa da Sadad wanda galin jama'ar garin Kiristoci ne.

Garin na tazarar kilomita 20 daga babbar hanya mai muhimmanci wadda ta hade Damascus babban birnin kasar da birnin Homs.