Syria:IS suna amfani da mutane don garkuwa

Hakkin mallakar hoto AP

Wani hoton bidiyo da aka wallafa ya nuna mutane maza da mata a cikin katon keji na karfe a bayan manyan motoci suna tafiya a hankali akan tituna.

Daya daga cikin wadanda aka kama din yace shi babban jam'in soja ne ya kuma yi roko a dakatar da luguden wutar da aka yi a yankin.

Faifan bidiyo ga alama ya fito ne daga yankin da yan tawayen suke da karfi a wajen Damascus inda harin roka ya hallaka mutane saba'in a wata kasuwa a ranar Juma'a.