Turkey:Jam'iyyar AK ta sami rinjaye a zabe

Hakkin mallakar hoto Reuters

Firaministan Turkiya Ahmet Davutoglu ya ayyana samun nasarar jam'iyyarsa ta AK mai mulki a zagaye na biyu na zaben majalisun dokoki.

Ya shaidawa taron magoya baya wadnad ke daga tutoci suna murna da annashuwa a mahaifarsa sa dake garin Konya a tsakiyar Turkiya cewa zaben nasara ce ga jama'ar Turkiya baki daya.

" Yace dole ne na gode muku jama'a ta. Wannan nasarar ba ta mu bace kadai nasara ce ta dukkan jama'ar mu da makota da kuma dukkan yan kasa. Muna godiya ga dukkan wadanda suka taimaka wajen samun wannan nasarar"

Yayin da kawo yanzu aka kidaya kusan dukkan kuri'un, jam'iyyar ta AK ta sami kusan kashi hamsin cikin dari na kuriun da aka kada.turkey