Ana zaben 'yan majalisu a Turkiyya

Kusoshin jam'iyyar AK, Mr Erdogan da Ahmet Devutoglu Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kokarin kafa gwamnatin hadaka ya ci tura a kasar Turkiyya.

A karo na 2 cikin watanni 5, al'umar kasar Turkiyya na kada kuri'a a zaben 'yan majalisu.

Jam'iyyar AK wadda shugaba Racep Tayyip Erdogan ya kafata, ta gagara kawo kujeru a zaben da aka yi a watan Yunin da ya wuce, haka kuma kokarin kafa gwamnatin hada a wancan lokacin ya ci tura.

Matsalar tsaro a kasar na sahun gaba abatutuwan da aka fi damuwa da su, tun bayan da aka rusa yarjejeniyar tsagaita wuta da tada kayar baya na Kurdawa da mayakan IS.

Shugaba Edogan ya yiwa al'umar kasar Turkiyya alkawarin tabbatar da zaman lafiya, idan har suka sake zabar jam'iyyarsa ta AK.

Ya yin da 'yan adawa ke gargadin cewa matukar jam'iyyar ta sa mu nasarar lashe kujerun majalisar kasar, to sai yadda hali ya yi.