Za a rage kaifin kutsen bayanai a Birtaniya

Image caption Theresa May, Sakariyar harkokin gida ta Birtaniya

Bisa sabon kundin dokar tsaro ta gwamnatin Birtaniya, 'yan sanda za su iya fahimtar adreshin intanet da mutane suka ziyarta amma ba za su gano takamaiman shafin da mutanen suka shiga ba, har sai sun sami iznin gano hakan.

Sakatariyar harkokin cikin gida ta Birtaniya, Theresa May ta ce kudirin da ya ba da damar bincike ba zai kunshi sassa masu haddasa kace-nace ba, irin na dokar tsaro ta 2012.

Ta ce an cire duk wasu sassa masu cike da rudani daga kudirin dokar na 2012, bayan sauraron korafe-korafen kungiyoyin da ba na gwamnati ba.

Sai dai kuma sakatariyar ta shaida wa BBC cewa akwai bukatar samun sammace wajen sanya ido kan al'amuran masu ta'ammali da intanet.

Amm kungiyoyin kwadago sun ce alkalai ne kawai ya kamata su amince da bayar da sammace ba 'yan siyasa ba.

Sabon kudurin dokar dai wanda za a gabatar wa majalisar dokokin Birtaniyar ranar Laraban nan wani yunkuri ne na baya-bayan nan da nufin sabunta dokar da ta ba wa 'yansanda da sauran jami'an tsaro damar yin kutse cikin intanet domin gano irin batutuwan da mutane kan tattauna akai.

Image caption Sabon kudirin dokar yana son tsaurara sha'anin tsaro a Birtaniya

Idan dai har hakan ya tabbata to jami'an tsaron za su iya fahimtar wane adreshi ko kuma website mutum ya shiga amma ba za su gano takaimaiman shafin da ya shiga ba.