Ministoci biyar da za a zuba wa ido a gwamnatin Buhari

Image caption Muhammadu Buhari ya kwashe watanni hudu ba tare da nada ministoci ba.

Daga karshe dai 'yan Najeriya sun san mutanen da Shugaba Muhammadu Buhari, zai rantsar a matsayin ministoci, bayan majalisar dattawan kasar ta tantance mutane 36, watanni biyar bayan shugaban ya hau kan mulki.

Sai dai mutane da dama ba su ji dadin ganin sunayen wasu daga cikin ministocin ba, bayan sun bata tsawon lokaci suna jiran a fitar da sunayen.

Wasu na cewa ministocin na cikin 'yan siyasar da aka hada baki da su wajen haifar da matsalolin da kasar ta fada a ciki.

Matasa -- wadanda suka jajirce domin ganin Buhari ya ci zabe -- ba su ji dadin tsarin da aka bi wajen nada ministocin ba.

Kazalika, kungiyoyin mata sun nuna rashin jin dadinsu, ganin cewa mata shida ne akwai a cikin ministocin

Ministocin guda 36 - wadanda har yanzu ba a ba su mukamai ba - sun hada da tsofaffin gwamnoni guda biyar, lauyoyi guda tara, tsofaffin 'yan majalisar dattawa guda hudu, malaman Jami'o'i guda uku, likitoci biyu, tsofaffin sojoji guda biyu, da malamin addini.

Hada 'yan siyasar da suka goge da kuma kwararrun ma'aikatan gwamnatin da masana a cikin gwamnatin Buhari ya nuna cewa shugaban yana so ne ya saka wa 'yan siyasa a kan goyon bayan da suka ba shi, sannan ya sanya kwararru a cikin tafiyarsa.

Masu goyon bayansa sun ce ya yi hakan ne domin ya cika alkawuran da ya dauka a lokutan yakin neman zabe, suna masu cewa batun "shekaru" da kuma "rashin mata da yawa" ba shi ne ke nuna alkiblar da gwamnatinsa ta dosa ba.

Kun san ministoci biyar da za a sa wa idanu?

Babatunde Fashola

Ba a yi mamakin ganin sunan Babatunde Fashola a cikin jerin sunayen ministocin ba.

Ayyukan da ya yi a lokacin da yake gwamna a jihar Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriya, sun sa ana ta yaba masa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Babatunde Fashola ya taka rawa wajen kawo sauye-sauye a jihar Lagos.

Ya yi aiki tukuru wajen kawo tsari a birnin na Lagos wanda yake a cunkushe gabanin hawansa mulki, inda ya rushe gine-ginen da aka yi ba a kan ka'ida ba, sannan ya yi gine-gine masu inganci cikinsu har da hanyoyi.

A matsayinsa na gogayyen lauya, ba za a yi mamaki ba idan aka ba shi mukamin ministan Shari'a ganin yadda Shugaba Buhari ya sha alwashin magance matsalar karbar hanci da rashawa da ta zama ruwan-dare a kasar.

Ibe Kachukwu

Shugaba Buhari ya nada Ibe Kachikwu -- tsohon babban jami'i a kamfanin mai na ExxonMobil -- a matsayin shugaban babban kamfanin mai na kasar, NNPC a watan Agusta domin magance cuwa-cuwar da ta yi kamari a kamfanin man.

Masu sharhi da dama na ganin cewa nadin nasa ya fara haifar da-mai-ido.

Sai dai mutane na mamakin yadda aka nada shi minista, ko da ya ke ana sa ran shi ne zai zama karamin ministan man fetur, bayan Shugaba Buhari ya ce shi ne zai zama babban ministan ma'aikatar.

Ana ganin shi ne zai rika kula da ma'aikatar dungurungun.

Yanzu dai akwai bukatar nada wani mutumin domin ya shugabanci babban kamfanin mai na kasar.

Amina Mohammed

Ta yi suna sosai a ciki da wajen Najeriya a matsayinta na kwararriyar ma'aikaciyar gwamnati.

Ta kwashe fiye da shekaru 30 tana yin aiki a fannonin ci gaba, cikin su har ta taba zama mai bai wa tsohon shugaban Najeriya shawara a kan muradun karni (MDGs).

Hakkin mallakar hoto Legis TV
Image caption Amina Mohammed ta goge sosai a kan muradun ci gaban kasashe.

An sallama mata wajen tsara hanyoyin ci gaban gwamnatoci da dama a kan yadda za a rage talauci.

Kafin a nada ta a matsayin minista, Hajiya Amina Mohammed ita ce ke bai wa Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon shawara kan sababbin muradun ci gaban kasashe.

Rotimi Amaechi

Shi ne mutumin da ya fi jawo cece-kuce a cikin mutanen da aka nada a mukaman ministoci, ko da ya ke nadin nasa bai zo wa kowa da mamaki ba.

Shi ne shugaban kwamitin yakin neman zaben Shugaba Buhari, kuma 'yan Najeriya da dama na kallon nadinsa a matsayin rawama kura aniyarta saboda rawar da ya taka.

Hakkin mallakar hoto Amaechi Twitter
Image caption Rotimi Amaechi yana da magoya baya sosai a yankin Naija delta mai arzikin man fetur.

Sai dai mutanen da dama sun soki nadinsa saboda zargin da ake yi masa da hannu a karbar hanci da rashawa lokacin da yake gwamnan jihar Ribas.

Amaechi ya sha musanta zargin, yana mai cewa yarfen-siyasa ne kawai.

Hasalima, ya kai gwamnatin jihar kotu kan rahoton da ta fitar da ke zarginsa da hannu a karabar hanci.

'Yan jam'iyyar hamayya sun yi kokarin ganin ba a tantance shi domin zama minista ba, amma hakarsu bai cimma ruwa ba.

AbdulRahman Dambazau

Shi ne Hafsan Hafsoshin rundunar sojin Najeriya tsakanin shekarar 2008 zuwa 2010, inda ya yi kokari sosai wajen ganin an murkushe kungiyar Boko Haram.

Bayan an kore shi daga aiki, kungiyar ta Boko Haram ta kara kaimi a shekarar 2011, kuma tun daga wancan lokaci, mayakanta sun kashe dubban mutane a Najeriya, sannan suka matsa kai hare-hare har makwabtan kasashe.

Shugaba Buhari ya sanya yaki da Boko Haram a cikin manyan bukatunsa, don haka watakila zai dora wa Janar Dambazau nauyin gudanar da wannan gagarumin aiki idan ya nada shi a mukamin ministan tsaron kasar.