Ana binciken sanadiyyar hadarin jirgin Rasha

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mutane na ci gaba da juyayi kan hadarin jirgin

Kamfanin jirgin saman Rasha da jirginsa ya yi hadari a yankin Sinai na kasar Masar, inda mutane 224 suka rasu, na cewa wani abu da ya faru daga wajen jirgin saman ne kadai, ake ganin zai kasance musabbabin hadarin.

A lokacin wani taron manema labaru a Masko, mataimakin daraktan kamfanin na Metrojet, Alexander Smirnov ya kawar da yuwuwar tangardar na'ura, yana mai cewa wani abu ne daga wajen jirgin saman za a iya dangantawa da hadarin na ranar Asabar.

Mai magana da yawun shugba Putin, Dmitry Peskov ya ce shugaba Putin zai gana da ministan sufurin kasar wanda ya je wajen da jirgin ya fadi domin yi masa bayani.

Mr Peskov ya fadawa BBC cewa ana ci gaba da bincike a kan musabbabin faduwar jirgin, amma ya yi gargadi kan yada jita-jita kan cewa 'yan ta'adda ne suka harbo jirgin.

Yanzu haka an kai gawarwakin mutane sama da dari da arba'in zuwa birnin St Petersburg.