Boko Haram: Eto'o na so a tallafa wa 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto Boko Haram Twitter
Image caption Miliyoyin mutane ne suka gudu daga gidajensu sakamakon hare-haren 'yan Boko haram.

Daya daga cikin fitattun 'yan kwallon kafar Afirka Samuel Eto'o ya yi kira da a kafa wata gidauniya da za ta tallafa wa mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa a kasashen Najeriya da Kamaru.

Eto'o ya yi gargadin cewa rashin tallafa wa mutanen zai ta'azzara matsalolin da yankin yammacin Afirka ke ciki.

Dan kwallon, wanda sau hudu yana zama zakaran kwallon kafar Afirka, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, "Akwai rikice-rikice daban-daban a yanzu haka. Da alama ba a lura da mutanen da suka rasa gidajensu a Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Nijar da kuma Najeriya ba".

Ya kara da cewa, "'Yan gudun hijirar da ke zaune a sansanoni sun karu daga 6,000 zuwa 50,000 a kasa da shekara daya, kuma hakan yana nufin wannan babbar matsala ce."

Hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram suka kwashe fiye da shekaru shida suna kai wa -- musamman a arewacin Najeriya -- sun raba mutane fiye da miliyan biyu da gidajensu, sannan sama da mutane 160,000 ke neman mafaka a Jamhuriyar Nijar da Kamaru.

Kazalika, hare-haren da kungiyar ke kai wa a kan iyakokin Najeriya da Jamhuriyar nijar da Kamaru sun raba mutane 80,000 daga gidajensu a yankin Arewa mai nisa na Kamaru, cikin shekara daya kawai.