An yi wa wata mata rajamu a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana yi wa wata mata bulala a Afghanistan

An yi wa wata mata ta rajamu inda ta mutu har lahira a tsakiyar Afghanistan bayan an zarge ta da yin zina.

Rahotanni sun ce an yi wa Rokhshana auren dole, amma kuma sai ta yi kokarin ta gudu da wani mutumin sa'anta wanda shi ma aka yi wa bulala.

An rarraba bidiyon lokacin da ake yi mata rajamu a wayoyin salula.

Gwamnan lardin, Seema Joyenda ta ce shugabbani addinni da wasu kungiyoyin masu tayar da kayar baya suna cikin mutanen suka aiwatar da hukuncin.

Ta bukaci gwamnatin kasar ta dauki wani mataki a kan wadanda suka aiwatar da hukuncin inda ta yi zargin cewa mutane a kauyukan na azabtar da mata.