Kamaru ta ki sakin dan jaridar da ke bincike kan BH

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban kasar Kamaru Paul Biya

Gwamnatin Kamaru ta bayyana cewa ta ki sakin wakilin sashen hausa na gidan rediyon Faransa RFI Ahmed Abba wanda jami'an tsaro suka kama watanni uku da suka gabata saboda ana gudanar da bincike a kansa.

Kakakin gwamnatin kasar Issa Tchiroma Bakary ne ya sanar da hakan, bayan kungiyar Amnesty International ta wallafa wani rahoto a kan kama dan jaridar.

Kakakin gwamnatin ya ce tsawon lokacin da aka dauka a ana tsare da Ahmed Abba, bayanai ake samu a wajensa, kuma hakan bai sabawa doka ba domin dokar yaki da ta'addanci a kasar ta tanadi hakan.

Issa Tchiroma Bakary ya kara da cewa, bai kamata wani ya ziyarce shi ba a yayin da yake tsare ake kuma gudanar da bincike a kansa, har sai an kammala samun bayanai.

Kungiyar Amnesty ta ce tun a shekarar 2014 mahukunta a Kamaru su ka kama mutane fiye da dubu guda wadanda ta ke zargi da goya wa kungiyar boko haram baya.