'Yan sanda sun kashe barayin shanu a Kano

Hakkin mallakar hoto AFP

Rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke arewacin Nigeria ta ce jami'anta sun kashe mutane uku da ake zargi masu satar shanu ne, a yayin musayar wutar da bangororin biyu suka yi.

Rundunar ta kuma ce an kwantar da mutane uku da suka samu raunuka a lokacin arangamar, sannan kuma aka kama wasu mutane tara.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Kano Muhammad Musa Katsina ya shaida wa BBC cewa sun kwato daruruwan shanu da bindigogi a wani yunkuri na fatattakar barayin shanu da rundunar ta ce ta dukufa a kai.

Matsalar satar shanu na daga cikin matsalolin da ake fuskanta ta fannin tsaro a yankin arewacin Najeriya, lamarin da kan janyo asarar dukiya da kuma rayuka.