Jama'a na cikin tasku a Gwoza ?

Hakkin mallakar hoto BOKO HARAM
Image caption Mazauna garin Gwoza sun ce har yanzu ana kai hare-hare

A Najeriya, ana samun karin bayanai game da yadda rayuwa take kasancewa a wasu daga cikin yankunan da sojoji suka kwato daga hannun 'yan Boko Haram.

Wasu mutane da suka fito daga Gwoza, sun ce mutane na rayuwa cikin kunci a garin, kuma har yanzu akwai rashin tsaro sakamakon hare-haren da Boko Haram ke ci gaba da kai wa a yankin.

Mazauna garin sun yi korafin rashin kayan masarufi da tsadarsu.

Kazalika, sun shaida wa BBC cewa 'yan siyasar da suka zaba sun guje su tun bayan kammala zaben shekarar 2015.

Sai dai kakakin rudunar yaki da Boko Haram ta 'zaman lafiya dole' da ke arewa maso gabashin Nigeria, Kanar Tuku Gusau, ya musanta zargin, kuma ya ce ba za ta yiwu a ce sojoji su na ko'ina ba.

Dangane da zargin da mazauna yankin suke wa 'yan siyasar su kuwa, Sanata Mohammed Ali Ndume ya bayyana cewa babu kanshin gaskiya a cikinsa.