Iyalan Sarki Fahd za su biya 'matarsa' kudi

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Janan Harb ta ce sun yi aure da Sarkin ne a shekarar 1968

Wata mata wacce ta ce sun yi auren sirri da da margayi tsohon sarkin Saudiyya, Fahd, ta samu nasara a shari'ar da ta shigar a wata kotu a London.

Matar wacce 'yar asalin Palasdinu ce mai suna Janan Harb, ta ce sun yi aure ne a shekarar 1968 lokacin Fahd yana yarima mai jiran gado.

Ta ce dan Sarki Fahd, Yarima AbdalAziz Bin-Fahd ya yi alkawarin lura da ita har tsawon rayuwarta kafin ya canza magana.

Sai dai Yariman ya musanta hakan.

Mai shari'a, Peter Smith ya ce akwai kanshin gaskiya a kan batun da matar watau Janan Harb ta ce, sun hadu da Yarima Abdul Aziz a wani otal a London lokacin Sarkin yana cikin tsananin ciwo, shekaru biyu kafin rasuwar sarkin a shekara ta 2005.

Alkalai a London sun ce akwai gaskiya a maganarta kuma dole ne a bata dala miliyan 23 da kuma gidaje biyu a London.

Dole ne Yarima AbdulAziz ya biya kudaden cikin makonni hudu ko kuma ya daukaka kara.

Sarki Fahd dai ya mulki Saudiyya ne daga shekarar 1982 zuwa 2005.