Shell ya yi karya a kan tsaftace muhalli

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yankin Niger Delta

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International da wata cibiyar kare muhalli, Centre for Environment, Human rights and Development sun zargi kamfani Shell da yin karya wajen tsaftace muhalli a yankin Niger Delta na Najeriya.

Kungiyoyin sun bayyana haka ne a wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar.

Sun ce binciken da suka yi ya nuna cewa akwai wurare da dama da mai ya gurbata a Najeriya, wadanda kuma kamfanin Shell din ya yi ikirarin sharewa tun 2011.

Kazalika, kungiyoyin sun soki hukumar sa ido a kan malalar mai ta Najeriya, suna masu zargin cewa tana ayyana wasu wurare a matsayin wuraren da aka kwashe man da ya malala alhali kuwa maganar ba haka take ba.

Kungiyoyin sun bukaci a kara kudin da ake samar wa hukumar, sannan a kara karfafa mata iko wajen sa ido a kan muhali.

Shell ya yi raddi

Sai dai a wata sanarwa da kamfanin na Shell ya fitar, ya musanta zargin, yana mai cewa yana share wuraren da gurbacewar muhallin ta shafa.

A cewar sa, " A shirye muke mu share dukkan wuraren da suka gurbata sanadiyar ayyukanmu komai tsadar yin hakan. Kazalika, muna share wuraren da suka gurbata a yankin Ogoniland duk da yake mun daina hoka mai a yankin tun daga shekarar 1993".