'Ya kamata a yi bayani kan asusun Nigeria'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ezekwesili ta ce gwamnatin Jonathan ta yi watsi da damar da Najeriya ta samu.

Tsohuwar ministar ilimi ta Najeriya, Oby Ezekwesili, ta bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari ya wallafa cikakken bayani kan halin da "asusun gwamnati" ke ciki domin 'yan kasar su san barnar da gwamnatocin baya suka yi.

Mrs Ezekwesili, wacce ta bayyana hakan a shafinta na Twitter, ta kara da cewa gwamnatin da ta wuce ta yi watsi da damar da kasar ta samu a shekaru biyar din da suka wuce lokacin da farashin man fetur ke da daraja.

Ta ce, "Ina bai wa masu tsara tattalin arzikin Najeriya shawara cewa a baje komai a faifai dangane da halin da asusun gwamnatin tarayya ke ciki, ta yadda kowa zai san halin da kasar nan ke ciki".

Ta kara da cewa hakan ne zai sa 'yan kasar su daura damarar fuskantar mawuyacin hali, kana masu yin sharhi kan tattalin arziki su san halin da ake ciki domin su daina yin tsokaci kan abubuwan da ba su da ilimi a kansu.

Tsohuwar ministar ta ce halin tabarbarewar tattalin arzikin da Najeriya ke ciki zai bayar da dama ga gwamnati ta kawar da kanta daga man fetur domin bunkasa sauran hanyoyin tattalin arziki.