Bayani kan mutanen da suka mutu a jirgin Rasha

Masana na yin bincike kan wasu tarkace da suka gani a kusa da wurin da jirgin ya fadi.

Asalin hoton, epa

Bayanan hoto,

Masana na yin bincike kan wasu tarkace da suka gani a kusa da wurin da jirgin ya fadi.

Hukumomi a kasar Rasha sun ce sun fara gano sunayen mutanen da suka mutu a hatsarin da jirgin kasar ya yi a Masar.

Mataimakin gwamnan St Petersburg, Igor Albin, ya ce iyalan mutanen sun gano mutane tara bayan da suka duba gawarwakinsu.

Dukkan mutane 224 da ke cikin jirgin da ya yi hatsari a yankin Sinai sun mutu.

An fara gudanar da bincike kan akwatunan adana bayanan jirgin guda biyu da aka tsinto.

Kamfanin dillancin labaran Rasha (TASS) ya ce masana na gudanar da bincike kan wasu tarkace da aka gani a kusa da wurin da jirgin ya fadi.

Tun da fari dai, Shugaba Abdul-Fattah al-Sisi na kasar Masar ya bayyana ikirarin da kungiyar IS mai ikirarin kishin Musulinci ta yi cewa ita ce ta harbo jirgin a matsayin "farfaganda".