Koriya ta kudu ta lashe gasar bidiyo ta bana

Yan wasan bidiyo ta Kwamfuta na kasar Koriya ta kudu watau SKT1 sun lashe gasar bidiyo ta bana da aka yi a birnin Berlin na kasar Jamus.

Yan wasan za su raba dala miliyan daya da za a basu sakamakon nasarar da suka yi.

Yan wasan sun doke kungiyar Koo Tigers da suma suka fito daga kasar Koriya ta kudu a wasan da aka yi gaban magoyan bayan gasar wasan bidiyo dubu goma sha biyar.

Kungiyar SKT1 ta samu galaba akan kungiyar Koo Tigers da ci uku da daya a zagayen karshe na gasar.

"A baya mun kara a kungiyar Koo kuma duk da cewa sun shahara a wanan wasa amma mun yi la'akari da cewa ba bu wani sauyi a yadda suke wasa a cikin shekara guda" a cewar Gyeong-hwan Jang daga kungiyar SKT1.