Jami'oin Afirka sun yi taro a kan Boko Haram

Image caption Rikicin Boko Haram ya raba dubban mutane da gidajensu

A jihar Diffa ta Jamhuriyar Nijar, jami'o'in kasashen Afirka akalla 20 ne suka yi taro domin yin nazari kan yadda za a magance matsalar kungiyar Boko Haram a kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi.

Taron, wanda Jami'ar garin Diffa ta shirya, ya bukaci masu ruwa-da-tsaki da su hada gwiwa domin magance wannan matsala da ke neman ta gagari-kundila.

Shugaban Jami'ar Maiduguri, Farfesa Aliyu Abubakar ya shaida wa manema labarai a wajen taron cewa, "Muna duba yadda za a iya bayar da shawarwari a kan yadda wadannan kasashe ( Nigeria da Nijar da Kamaru da Chadi) za su hadu domin su magance matsalar".

Ya kara da cewa, "Harkar tsaro ba harka ce kawai ta soji ba, harka ce wacce ta shafi kowa da kowa; saboda haka ne kasashen nan da kuma Jami'oin da ke kasashen suka taru saboda a tattauna a ga inda za a samu mafita".

Shugaban Jami'ar Diffa ya shaida wa BBC cewa sun shirya wannan taro ne bisa la'akari da kiraye-kirayen da al'ummar jihar ke yi musu na neman hanyoyin da za a kawo karshen matsalar.