'Yancin siyasa zai dauki lokaci — Sisi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu na kallon Al-Sisi a matsayin mai kama karya

Shugaba Abdel Fatah Al-Sisi na Masar ya ce kasar na kan tafarkin demokradiya, sai dai samar da 'yancin siyasa zai dauki lokaci.

A wata hira da ya yi da BBC, Shugaba Sisi wanda ya karbi mulkin kasar shekaru biyu da suka wuce daga shugaba Mohammed Morsi wanda ya yi mulkin farko a karkashin demokradiya a Masar, ya ce ba a yi adalci ba, idan har aka kwatanta tarihin demokradiyyar kasar da ta kasashen Turai.

Ya ce yawancin Misrawa suna jin tsoron tsatsaurar ra'ayin Musulunci da kuma rashin tsaron da ake fuskanta a wasu lardunan.

Wani wakilin BBC ya ce wasu suna ganin shugaba Sisi a matsayin jarimin shugaba da Masar ke bukata, amma kuma wasu suna yi masa kallon dan kama karya.

Mr Sisi wanda zai kai ziyara Biritaniya cikin wannan makon, ya ce ya gudanar da zabe cikin walwala da kuma adalci sannan kuma 'yan Masar ba za su kara bari a yi musu mulkin kama karya ba.