Masar: Jirgin kasa ya makale tsawon shekaru tara

Image caption Jirgin kasan Masar a tsaye

Wani kamfanin dakon kaya a kasar Masar ya fara aikin kokarin ciro wani jirgin kasa da ya makale kusan shekaru tara da suka gabata a wani kasurgumin daji.

Jirgin dai ya kasa motsawa daga tasharsa ta Kharga saboda wasu matsaloli da suka shafi satar kwangiri (layin dogo) na wani bangare da jirgin ya kamata ya hau.

Matsaloli na layin dogon na daga cikin abubuwan da suka hana jirgin motsawa daga inda yake.

Yanzu haka dai injiniyoyi sun fara kwankwance jirgin tare da dora shi a cikin manyan motoci.

Da farko dai 'yan sanda sun kama injiniyoyin suna zaton ko barayi ne.