Boko Haram: Soji sun yi raddi kan ƙera makamai

Hakkin mallakar hoto Contributor
Image caption Boko Haram ta nuna yadda mayakanta ke ƙera makaman roka.

Rundunar sojin Najeriya ta ce kungiyar Boko Haram ta nuna yadda mayakanta ke ƙera makaman roka ne domin cusa tsoro a zukanta 'yan ƙasar.

Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce, "Boko Haram ta fitar da hotunan ƙera makamanta ne domin ta sanya fargaba a zukatan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba sannan ta nuna cewa har yanzu tana da karfin gudanar da ayyukanta. Muna so mu tabbatar wa mutane cewa wannan barazana ce kawai".

Ta kara da cewa, "Hakan ya nuna cewa wadannan 'yan ta'adda makiyan Najeriya ne, kuma ya kamata mu hada gwiwa domin kawar da su".

Rundunar sojin ta ce dakarunta na bin matakai daban-daban domin ganin sun murƙushe ƙungiyar ta Boko Haram ba tare da hakan ya shafi fararen hula ba.