Ma'aikata a Nigeria sun koka kan albashi

Image caption Wasu 'yan Najeriya masu bin layi a banki

A Najeriya, ma'aikatan gwamnatocin wasu jihohi sun fara kokawa da jinkirin samun albashin watan Oktoba har zuwa wannan lokaci.

Ma'aikatan na cewa sun shiga mawuyacin hali sakamakon jinkirin biyansu albashin.

Ma'aikatan sun ce sakamakon rashin biyansu albashin, ba sa iya biyan kudin makarantar yaransu da kuma gudanar da harkokin yau da kullun.

Su ma wasu 'yan kasuwa musanman a jihar Kano sun ce matsalar ta shafe su, inda suke cewa al'amura sun tsaya musu cak, yayin da suma masu sana'a a harabar ma'aikatun gwamnati ke cewa kwantai kawai suke yi yanzu.

Sai dai wasu gwamnatocin na cewa jinkirin samun kason kudinsu daga gwamnatin tarayya da kuma koma-baya a kason kudin ne ya haifar da jinkirin albashin ma'aikatan.