Gini ya hallaka mutane 16 a Pakistan

Image caption Masu aikin ceto na ci gaba da ayyuka a masana'antar

Jami'ai a Pakistan sun ce a kalla mutane 16 ne suka mutu a birnin Lahore da ke kudancin kasar, sakamakon rugujewar wata masana'anta da ke birnin.

An kai mutane da dama wadanda suka jikkata asibiti kuma daruruwan wasu mutanen sun makale a baraguzan ginin.

Tuni dai tawagar masu bada agajin gaggawa suka kai injinan da za su fito da wadanda suka makale a baraguzan ginin.

Masana'antar wacce ke yin jukunkuna, ta na a yankin Sundar ne da ke wajen birnin Lahore.

Ko da ya ke ba san abin da ya haddasa ruftawar masana'antar ba, akwai yuwuwar girgizar kasar da aka yi a watan da ya gabata a Pakistan, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dari biyu da saba'in ce ta raunana ginin.