Google ya gano baraka a Galaxy S6 Edge

Image caption Wayar Samsung Galaxy S6 Edge

Google ya bayyana wasu matsalolin tsaro 11 da ya gano a babbar wayar Samsung Galaxy S6 Edge.

Matsalolin sun hada da wata baraka da ake gani masu kuste za su iya amfani da ita wajen sarrafa wayoyin Galaxy S6 Edge na mutanen da tsautsayi ya fada ma wa.

Sai dai kamfanin Samsung ya gyara akasarin matsalolin bayan da Google ya janyo hankalinsa akan su, amma har yanzu wasu matsalolin ba su gyaru ba.

Wani kwararre kan fasahar wayoyin salula, Dr. Steven Murdoch ya ce barakar ta yi tasiri sosai wajen kawo rauni a babbar manhajar Google a wayoyi.

Wani ayarin kamfanin Google da aka dora wa alhakin gano matsalolin da suka shafi tsaron kwamfutoci wadanda ba a san da su ba a baya ba, Google Project Zero ne ya gano matsalolin wayar ta Galaxy S6 Edge.

Ayarin ya ce bayan mako guda da fara sayar wayar Galaxy S6 Edge a watan Afrilu, ya gano barakar 11 da suka shafi tsaron wayar.

Daga cikin matsalolin da ayarin ya gano, har da wata baraka a manhajar aikawa da sakonnin Email wadda za ta bai wa masu kutse damar samun sakonnin masu wayoyin.

Wata matsalar kuma ita ce wadda ta ke bai wa masu kutse damar sukurkuta tsarin manhajar kallon hotuna a wayoyin.