Shugabannin China da Taiwan za su gana

Image caption Shugaba Xi Jing-ping da Ma Ying-jeou

Kasashen China da Taiwan sun ce suna fatan ganawar da shugabannin kasashen biyu za su yi mai cike da tarihi, za ta taimaka wajen rage zaman dardar a yankin.

Shugaban Xi Jin-ping na China da Ma Ying-jeou na Taiwan za su gana ranar Asabar a Singapore, a karon farko da shugabannin kasashen biyu za su tattauna cikin shekaru masu yawa.

Kasar Taiwan ta kasance mai mulkin kanta tun bayan yakin basasar kasar China a shekarar 1949, yayin da Chinan take yi wa Taiwan kallon wani yankinta da ya balle, wanda kuma wata rana zai sake komawa cikin Chinan.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta kara gwabi a lokacin shugaba Ma Ying-jeou wanda ake yi wa jam'iyyarsa ta KMT kallon mai dasawa da China.

Amurka -- wacce babbar kawar Taiwan ce -- ta ce ta yi marhabin da labarin tattaunawar da shugabannin biyu za su yi.