Akwai gyara a shugabancin Buhari — Yakasai

Image caption Tanko Yakasai ya ce Tsohon Shugaba Jonathan ya goya wa baya ba jam'iyyar PDP ba

A Najeriya, wani dattijon dan siyasa Alhaji Tanko Yakasai ya soki yadda shugaban kasar Muhammadu Buhari ke tafiyar da al'amuran kasar.

A hirarsa da BBC, Alhaji Tanko Yakasai ya yi zargin cewa wasu manufofin da Shugaba Buhari ya bullo da su da kuma salon yaki da cin hanci da matsalar tsaro, abubuwa ne da suke barin baya-da-kura.

Dattijon dan siyasar ya ce bai kamata a dauki kusan watanni biyar ba a nada ministoci ba, kuma hakan ya sa ayar tambayoyi a zuciyarsa.

Ya ce, "Lokacin kamfe kowa ya san ban goyi bayansa ba kuma yanzu bayan ya hau kan mulki na yi fatan ya yi nasara, domin idan ya yi nasara ina cikin wadanda za su ci moriya, idan kuma bai yi ba, ina cikin wadanda za su cutu."

Alhaji Tanko Yakasai ya kara da cewa yana bai wa shugaban Nigeria shawara ta kafar jarida kuma yana fatan Shugaba Buhari zai dauki shawarwarinsa.

Sai dai fadar Shugaban Nigeria ta mayar da martani inda mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ya ce ba za su yi jayayya da Alhaji Tanko Yakasai ba a matsayinsa na daya daga cikin dattijan kasar.