Sanatoci sun ki amincewa a bai wa 'yan Nigeria N5,000

Image caption Jam'iyyar APC ta yi alkawarin bai wa matasan da ba su da ayyukan yi N5,000 duk wata.

'Yan majalisar dattawan Najeriya sun yi watsi da kudurin dokar da ya bukaci gwamnatin tarayya ta rika bai wa matasan da ba su da ayyukan yi N5,000 duk wata.

Yawancin sanatocin da suka ki amincewa da kudurin dokar 'yan jam'iyyar APC mai mulki ne.

Takwarorinsu na jam'iyyar adawa ta PDP sun goyi bayan kudirin, sai dai ba su samu cikakken goyon bayan da zai sa a amince da kudirin ba.

Sanata Philip Aduda na jam'iyyar PDP ne ya gabatar da kudirin.

Jam'iyyar ta APC dai ta yi alkawarin bai wa matasan da ba su da ayyukan yi N5,000 a duk wata, a lokacin da take yakin neman zabe.

Sai dai wasu na ganin da wuya ta iya cika wannan alkawari saboda mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.