'Mun samu galaba kan Boko Haram'

Image caption Wasu daga cikin ministocin Nigeria

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya ce ko a haka sojojin kasarsa sun daidaita mayakan kungiyar Boko Haram kuma ba za su yi kasa a gwiwa har sai sun ga bayanta ga baki daya.

Ya bayyana haka ne a yayin bude taron horarwa na kwanaki biyu da ya shirya wa sabbin ministocinsa a fadarsa da ke Abuja.

Shugaba Buhari ya ce wannan ne ya sa sauran 'yan kungiyar Boko Haram da suka rage, suka shiga kai hari kan mutane da wuraren da ba su da kariya.

'' Zabe na a matsayin shugaban wannan kasar ya ta'allaka ne kan alkawura uku da na yi na yakar cin hanci, da rashin tsaro da kuma farfado da tattalin arziki," in ji Buhari.

Ya kara da cewar "Mun riga mun dauki kwararan matakai na toshe kofofin da ake satar kudin gwamnati da arzikin kasa. Kuma dukanku kun san irin matakan da muka dauka wajen maganin kungiyar Boko Haram."

Maudu'ai biyar ne dai za a yi wa sabbin ministocin bita a kai a cikin wadannan kwanakin biyu da suka hada da sanin abin da ake nufi da aiki gwamnati da kuma yadda za a shi yi dai dai.

Image caption Shugabar ma'aikata Winifred Ita Eyo;da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; da kuma shugaba Muhammadu Buhari

Sauran su ne yadda minista zai nisanta kansa daga shiga uku da kuma alkiblar gwamnati kan yaki da cin hanci, da yadda tsarin tarayyar kasar yake, da ka'idojin da'ar ma'aikata da kuma inda aka dosa kan batun farfado da tattalin arziki.