Na fi kowa iya kwallo a duniya - Ronaldo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ronaldo ya ce ya fi Messi kwarewa a kwallo.

Dan kwallon Real Madrid Cristiano Ronaldo, ya ce shi ne dan kwallon da yafi kowa a duniyar kwallo ta yanzu, kuma za a iya kwatantashi ne kawai da wadanda suka fi kowa fice a tarihin kwallo.

A wata hira da ya yi da BBC, ya ce ya kai wani mataki a kwallo da zai yi wahala a ce yana bukatar kara kaimi.

Dan kwallon dan kasar Portugal mai shekara 30, sau uku yana lashe gasar dan kwallon da ya fi kowa a duniya, kuma shine wanda ya fi kowa yawan cin kwallo a wannan zamani.

Ronaldo ya ce: "Bana bukatar sai na ce ni tarihi ne a kwallo, ko ni ne gwarzo. Wadannan nasarori nawa kawai sun isa shaida."

Ronaldo, wanda ya koma kulob din Real Madrid daga Manchester United a shekarar 2009 kan kudi pam miliyan 80, ya ce ya kai wani matsayi marar misaltuwa a wasan kwallo cikin shekaru takwas da suka gabata, kuma yana son ci gaba da buga wasa na tsawon kakar wasanni biyar ko shida.

Da aka tambaye shi kan in aka kwatanta shi da dan wasan Barcelona Lionel Messi kuwa, sai Ronaldo ya ce "Wanna kuma ra'ayi ne, watakila a ra'ayinku Messi ya fi, amma ni dai a wajena na san na fi shi, Fakat."

Dan wasan dai ya buga wasanni 760 tun farkon shigarsa kwallon kafa inda ya ci kwallaye 504.