Rasha da Masar sun kalubalanci Biritaniya

Image caption A kan faduwar jirgi a Sinai ake cece-kuce

Kasashen Rasha da Masar sun ce ba wata shaida da za ta tabbatar da ikirarin Biritaniya na cewa bam ne ya haddasa faduwar jirgin Rasha a yankin Sinai a ranar Asabar.

Pirai ministan Biritaniya, David Cameron ya kare matakin da gwamnatinsa ta dauka na hana jiragenta zuwa wajen shakatawa na Sharm-el-Sheikh wajen da jirgin ya taso.

Ya ce zai tattauna batun da shugaban Masar, Abdul Fatah al-Sisi amma kamar yadda ya ce tilas ne a saka batun kare lafiyar 'yan Biritaniya.

Masar ta ce ba a fada mata shawarar da Biritaniya ta yanke ba tun da wuri.

Gaba daya mutane 224 da ke cikin jirgin ne suka mutu.