Kasafin Najeriya na 2016 zai haura N7tr

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo

Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce aiki ya yi nisa wajen shirya gagarumin kasafin kudi na shekarar 2016, wanda ake gani zai kai naira triliyan 7 zuwa takwas.

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ne ya yi tsokacin a wajen taron bitar da aka shirya wa sabbin ministocin kasar 36.

Kasafin kudin kasar da aka shirya mna shekarar 2015, naira triliyan hudu ne da doriya, saboda haka, a kasafin na badi, za a samu gagarumin karin kudade.

Gwamnatin dai ta shirya aiwatar da gagarumin kasafin ne a daidai lokacin da kasar ke fama da rashin kudi.

Mallam Garba Shehu, kakakin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatin ta na so ta ware fiye da kashi 40 cikin dari domin gudanar da manyan ayyuka, sabanin a baya yadda akwa ware kimanin kashi 70 cikin dari ga ayyuka yau da kullun.

Ya ce gwamnati za ta nemo kudaden ne ta hanyar karbar haraji yadda ya kamata, da kuma wani asusu na hadin gwiwa da bangarori masu zaman kansu.