Ana ci gaba da aikin ceto a Brazil

Image caption Matsalar ta shafi kauyuka da dama

Mahukunta a kudu maso gabashin Brazil sun kwashe daruruwan mutane daga wani kauye da dagwalan hakar ma'adanai mai guba ya malale.

Ana fargabar akalla mutane 17 sun mutu bayan da wata madatsar ruwa da ke dauke da dagwalan wani kamfanin hakar sidaren karfe ya balle, inda ya shafe wasu kauyuka a kusa da wajen.

Wasu hotuna da aka dauka ta sama sun nuna jan ruwa da tabo da kuma gidajen da suka lalace ko wadanda suka nutse sai rufin kwano ake gani.

Madatsar ruwan dai, ta kasance wurin da ake tara dagwalon ma'adinai ne a yankin.