Direbobi sun rufe hanyar shiga Apapa

Wasu direbobin manyan motoci
Image caption Wasu direbobin manyan motoci

Direbobin manyan motoci da ke Apapa a jihar Legas ta Nigeria sun rufe hanyar shiga yankin da manyan motoci tare da yin zanga zanga.

Direbobin dai sun fara zanga zangar ne a daren Asabar sakamakon zargin sojoji na hadin gwiwa na Task Force da dukan wani direba da aka ce a yanzu haka yana cikin mumunan yanayi.

Wani jamiin kungiyar NARTO ya shaidawa BBC cewa ana zargin sojoji da tare direban motar akan sai ba su naira 500 amma sai ya mika masu 200.

Kungiyar ta NARTO ta ce sun sha kai kara gaban hukuma amma har yanzu matsalar bata sauya zani ba.