Za a cigaba da kwashe mutanen da ke Sharm el-Sheikh

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Masu yawon bude idanu sun yi carko-carko a Sharm el-Sheikh

A yau Asabar ne za a ci gaba da yunkurin kwashe dubban 'yan kasashen waje masu yawon bude ido a birnin Sharmul-Sheikh na kasar Masar, inda jirgin Rasha da ya yi hadari a makon jiya.

Rasha ta na tsara wani shiri na mayar da 'yan kasarta 45,000 zuwa gida.

Aikin kwashe masu yawon bude ido 'yan Burtaniya da suka makale a garin, da aka fara jiya ya gamu da matsaloli, bayan da hukumomi a Masar din suka ce filin jirgin saman ba zai iya daukar duk kan aikin gaggawa na kwashe masu yawon bude idon ba.

Dududu, takwas ne daga cikin jirage 29 da aka shirya zasu tashi zuwa Burtaniya daga Masar din, aka bari suka suka tashi.