Mai sayar da jarida da ya kona kansa ya rasu

Hakkin mallakar hoto AFP

Berenger Obame Ntoutoume mai shekaru 28 da haihuwa ya kona kan sa ne a ranar lahadin da ta wuce a wani ofishin 'yan sanda bayan da jami'an 'yan sandan suka kwace kayayyakinsa.

An ce ya rasu ne a sashen kula da masu tsananin jinya a asibitin sojoji dake Libreville babban birnin kasar.

Wannan shine karon farko da aka sami wani ya sanyawa kan sa wuta a Gabon.

Kafofin yada labarai na cikin gida sun ce 'yan sanda sun sha tsangwamarsa.

A watan Disambar 2010 ma wani mai sayar da jarida a kan titi a kasar Tunisia Mohammed Bouazizi ya jona kan sa kurumus domin nuna bacin rai da kwace masa kayayyaki, lamarin da ya haddasa tarzoma da zanga zangar juyin juya hali na kasashen larabawa a yankin.