Syria: IS ta sako wasu Christoci da ta kama

Mutanen suna daga cikin wasu mutane kimanin 200 da aka kama a arewa maso gabashin Syria a farkon wannan shekarar.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta yankin Assyria ta ce an kai mutanen garin Tal Tamr a gundumar Hasakeh.

Kungiyar IS ta yi garkuwa da daruruwan mutane a yankunan da ta kama a Syria da Iraqi.assyria