Yan bindiga sun kashe mutane tara a Burundi

Hakkin mallakar hoto AFP

Magajin garin birnin Bujumbura ya baiyana harin a matsayin kisan rashin imani.

Yace an tilastawa mutanen su kwanta a kasa sannan aka harbe su.

Kisan ya auku yayin da wa'adin da gwamnati ta baiwa yan bindiga su mika makaman su ko kuma su fuskanci hukunci ya cika.

Akalla mutane ashirin aka kashe Burundi a makon da ya wuce a irin kashe kashen da suka biyo bayan sanarwar shugaba Nkurunziza ta tsayawa takara karo na uku a karagar mulki.