An kai harin kunar bakin wake a Chadi

Yan kungiyar Boko Haram a kasar Chadi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yan kungiyar Boko Haram a kasar Chadi

A cewar majiyoyin tsaro a Ndjamena babban birnin Chadi yan kunar bakin waken mata biyu da wasu fararen hula biyu sun rasu a harin yayin da wasu mutanen 14 kuma suka sami raunuka.

Harin wanda aka dora alhakin sa akan yan kungiyar Boko Haram ya faru ne a kauyen Ngouboua dake kusa da iyaka da Najeriya.

Kauyen ya sha fuskantar hare haren Boko Haram tun bayan da suka kaddamar da hari a Chadi a watan Farairu.

Hare haren kunar bakin wake wadanda galibi ake amfani da manyan mata da yara mata kanana wajen kai wa na zama wani sabon salo da Boko Haram ta ke amfani da shi.

Tun farkon wannan shekarar sojojin Chadi sun zafafa farmaki akan Boko Haram wadda hare harenta suka yadu daga arewa maso gabashin Najeriya zuwa kasashen Chadi da Niger da kuma Kamaru dake makwabtaka da Najeriyar.