An gudanar da jana'aiza a Rasha

Jirgin Rasha da ya yi hadari a Masar. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Hukumomi na ganin cewa mayakan IS ayankin Sinai su ne suka dasa abin fashewa a cikin jirgin.

Ana gudanar da jana'iza a dandalin St Petersburg, na mutanen da suka rasa rayukansu a hadarin jirgin saman Rasha da ya fadi a yankin Sinai na kasar Masar.

Za a gudanar da addu'o'i na musamman, tare da kada kararrawa sau 224 adadin wadanda suka rasu, yawancinsu 'yan kasar ta Rasha ne.

Jami'ai a Rasha sun ce su na bin duddigin lamarin, dan gano musassabin faduwar jirgin. Sai dai sun ce su na kyautata zaton bam aka dasa a cikin jirgin.

Sai dai hukumomi sun ce za a iya daukar makwanni kafin a gama kwashe 'yan kasar Rasha da ke wurin shakatawar na Sharm el-sheikh.