Ana so a dakatar da Rasha daga wasannin tsalle-tsalle

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana zargin 'yan wasan tsalle-tsalle da guje-gujen Rasha da shan kwayoyi bna bisa ka'ida ba

Hukumar yaki da amfani da kwayoyin kara kuzari a wasanni ta duniya WADA, ta yi kira da a dakatar da Rasha daga wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya saboda yadda ake samun karuwar amfani da kwayoyi ba bisa ka'ida ba.

A wani rahoto da kwamitin hukumar mai suna WADA ya fitar, ya ce ana amfani da kwayoyin kara kuzarin da yardar hukumomin Rasha.

Hukumar ta bayar da shawarar cewa kamata ya yi hukumar da ke kula da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya, IAAF ta haramta wa wasu 'yan tseren kasar Rasha biyar da wasu kociyoyi biyar shiga wasanni har abada, inda ta kara da cewa 'yan tseren Rasha sun yi wa gasar Olympics da aka yi a London a 2012 kafar-ungulu.

Kazalika, hukumar ta jajirce cewa zai yi wuya a ce amfani da kwayoyin kara kuzari a wasanni ya takaita ga Rasha ko ga 'yan wasan tsere.

Hukumar 'yan sanda ta duniya ta ce za ta shirya wani bincike na duniya kan almundahana a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle.

A makon da ya gabata ne, masu shigar da kara na Faransa suka zargi tsohon shugaban hukumar wasannin da hannu a lamuran da suka shafi almundahana.

Ana zarginsa da karbar hanci domin lullube wasu rikice-rikice kan amfani da kwayoyin kara kuzari a wasanni da suka faru a Rasha.