Dasuki ya kai karar gwamnatin Nigeria

Hakkin mallakar hoto The Will
Image caption Tsohon mai ba wa shugaban kasa shawara kan tsaro, Sambo Dasuki

Tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara a kan harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki ya shigar da kara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, yana kalubalantar gwamnatin kasar da yin barazana ga rayuwarsa.

Kanar Sambo Dasuki mai ritaya ya bukaci kotun ta tilastawa gwamnatin tarayya -- musamman jami'an hukumar tsaron ta farin kaya -- da su gaggauta janye kawanyar da suka yi wa gidansa da ke Abuja.

Jami'an hukumar tsaron dai sun kwashe kwanaki biyar suna kewaye da gidansa.

Ana zargin Sambo Dasuki ne da laifin kin bai wa gwamnati hadin kai wajen yin bayani a kan badakalar kudi dalar Amurka miliyan dubu biyu da suka bace da sunan siyan makamai a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan.

A makon jiya ne wata kotu ta umarci hukumar tsaron farin kayan da ta ba wa Kanar Dasuki fasfo dinsa domin ya samu damar zuwa kasashen wajen inda za a duba lafiyarsa.