EFCC: Buhari ya sallami Lamorde

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tun da Buhari ya hau mulki ake maganar cire Lamorde

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya sallami shugaban hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasar Ibrahim Lamorde daga mukaminsa.

Shugaban ya kuma sanar da nadin Ibrahim Mustapha Magu a matsayin shugaban riko na hukumar ta EFCC.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na twitter, mataimaki na musamman ga shugaban Najeriya kan harkokin yada labarai, Mallam Garba Shehu, ya ce, sabon shugaban Hukumar ta EFCC Ibrahim Mustapha Magu, dan sanda ne mai mukamin mataimakin kwamishinan dan sanda.

Kuma zai rike shugabancin hukumar ne a matsayin na riko.

Sai dai sanarwar ba ta yi karin bayani kan dalilin da ya sa aka sauke mallam Ibrahim Lamorde daga mukaminsa na shugaban hukumar ta EFCC ba.

Amma a baya-bayan nan an zargi hukumar EFCC karkashin jagorancinsa da karkatar da wasu kudade da suka kai naira trilliyan daya zuwa wasu asusu na kashin kai.

A cewar wanda ya gabatar da wannan zargi a gaban majalisar dattawan kasar, an kwato kudaden ne daga hannun wasu mutane da ake zargi da yin sama da fadi.

Shi dai Ibrahim Lamorde ya musanta dukkanin wannan zargi a wata hira da ya taba yi da BBC inda ya ce hukumarsa na binciken shi kanshi wanda ya gabatar da zargin a gaban majalisar dattijan Nigeria da yin almundahana, a don haka maganar sa ba abin a yi amfani da ita ba ne a matsayin hujja.

A karshen shekara ta 2011 ne, Ibrahim Lamorde ya maye gurbin Misis Farida Waziri a matsayin shugaban EFCC a zamanin mulkin tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan.

Shugaba Buhari ya samu nasara a zaben shugaban kasar ne saboda alkawarin da ya dauka na cewar zai yi yaki da cin hanci da karbar rashawa a kasar.

Najeriya na da dimbin arzikin albarkatun kasa, amma cin hanci da rashawa sun sa ba a aiwatar da ayyukan ci gaban kasar dai-dai da kudaden haraji da kasar take samu.