Kotu ta hana Facebook sa wa mutane ido

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Idan Facebook bai bi umarnin kotun ba to zai biya tarar Yuro dubu 250

Wata kotu a Belgium ta ba wa Facebook sa'o'i 48 da ya dakatar da bincike kan mutanen da ba sa ta'ammali da kamfanin.

Facebook ya ce zai daukaka kara domin kalubalantar hukuncin.

Ya ce hukuncin kuma yana da alaka ne da tsoron tsarin da Facebook din yake amfani da shi na Cookies wanda yake gano iya yawan mutanen da suke amfani da shafukan intanet daban daban.

Ana kuma sanya shi wannan cookies din ne domin gano mutanen da suke ziyartar shafukan intanet ko da kuwa ba masu hulda da Facebook din ba ne.

Sai dai kuma kotun ta Belgium ta ce Facebook zai iya kalato bincike akan mutanen da ba masu huldatayya da su ba amma fa sai da izninsu.

Idan kuma Facebook din bai bi wannan umarnin ba to zai fuskanci tarar tsabar kudi har kusan Yuro dubu 250 a kowace rana.

Image caption Facebook ya ce zai daukaka kara

Kuma tarar za ta shiga lalitar hukumar kula da sirrin masu amfani da intanet wadda ita ce ta shigar da karar.