Nigeria na fama da karancin man fetur

Image caption Wurin da ake samun man ana sayar da shi kan Naira dari zuwa sama.

A Najeriya, an fara fuskantar karancin man fetur, inda dogwayen layukan mai suka dawo a gidajen mai na wasu jihohin kasar.

Hakan na faruwa ne kauwa duk da kokarin da hukumomin kasar ke cewa suna yi na samar da wadataccen man fetur.

Gidajen man suna sayar da lita daya a kan Naira dari zuwa sama.

Ana zargin dillalan man fetur masu zaman kansu da haifar da wannan matsalar.

Sai dai su ma 'yan kasuwar na cewa matsalar ta sha kan su.

Matsalar karancin mai dai a Najeriya na neman zama gagarabadau.

A makon jiya ne dai gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta amince da bai wa dillalan man fetur din Naira biliyan 413 na bashin da suke bi na tallafin mai.