India: Za a ci gaba da sayar da taliyar Maggi Noodles

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kwashe watanni biyar ba a sayar da taliyar Maggi Noodles a Indiya.

An dawo da sayar da daya daga cikin sanannun abinci na Indiya, wato taliyar Maggi Noodles, bayan da aka shafe fiye da watanni biyar ba a sayar da ita a kasuwa sakamakon gano cewa taliyar za ta iya cutarwa kuma tana da hadari.

Hukumomi a Indiya sun sanya dokar haramta sayar da taliyar suna mai cewa tana dauke da dalma da yawa. Amma kamfanin na Nestle a Indiya ya musanta hakan.

A yanzu dai an tabbatar da cewa za a iya ci gaba da amfani da taliyar Maggi Noodles.

An tilasta wa kamfanin lalata fakiti miliyan 400 na taliyar, inda suka yi asarar dala miliyan 70.