Dan Nigeria ya lashe gasar Scrabble

Gasar Scrabble ta hada kalmomi. Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Buhari ya ce Mista Jighere abin alfahari ne ga Nigeria.

Wani dan Najeriya ya zamo dan Afurka na farko da ya lashe gasar wasan dara na Scrabble na duniya.

Wellington Jighere mai shekaru talatin da biyu ya yi amfani da manyan kalmomi da suka fi bada maki irinsu Mentored da avouched da kuma fahlores wajan doke abokin wasansa bature, Lewis Mackay a wasan karshe da aka yi a birnin Perth na kasar Australia.

Mista Jighere ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa a lokacin da ayke wasan, ji yake tamkar nahiyar Afrika baki daya na bayansa ne.

Tuni Shugaba Muhammadu Buhari ya kira Mista Jighere ta wayar tarho ya taya shi murna. Ya kara da cewa hakika Mista Jighere abin alfahari ne ga Nigeria.

Kazalika, 'yan kasar ma da dama suna murnar wannan nasara ta Mista Jighere.

A watan Yuli wani dan kasar New Zealand, Nigel Richards, ya lashe irin wannan gasar ta kasashen da ke amfani da harshen Faransa, duk da cewa bai iya kalma daya ta faransanci ba.