Yaushe Buhari zai rantsar da ministoci ?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon gwamnan jihar Lagos, Babatunde Fashola na cikin ministocin da Buhari zai rantsar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai rantsar da ministocin da ya nada ranar Laraba.

Wata sanarwa da mai ba shi shawara a kan watsa labarai, Femi Adesina, ya sanya wa hannu ta ce za a rantsar da ministocin ne a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

A cewarsa, an bar kowanne minista ya halarci wajen rantsar da shi ya samu rakiyar mutanen da ba su wuce biyu ba.

Sai dai Adesina bai yi bayani kan ma'aikatun da aka bai wa kowanne minista ba.

A watan Satumba ne Shugaba Buhari ya nada ministoci 36, kana ya aike da su ga majalisar dattawan kasar domin ta tantance su.

Ministocin sun hada da tsofaffin gwamnonin jihohi da 'yan siyasa da kwararru a fannoni daban-daban na rayuwa.