Ce-ce-ku-ce kan sabon jirgin shugaban Afrika ta Kudu

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A kwanakin baya ne daliban jami'o'i a kasar suka yi zanga-zanga bayan da gwamnati ta ce ba za ta iya daukar nauyin biyan kudin karatunsu ba.

Gwamnatin Afrika ta kudu na shan suka kan shirin da rundunar tsaron kasar ke yi na saya wa shugaba Jacob Zuma sabon jirgi.

Rahotanni sun ce sayen sabon jirgi zai tatsi masu biyan haraji na kasar kimanin dala miliyan 280.

Babbar jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance, ta ce wannan shiri ba abinda za a amince wa ba ne musamman a lokacin da rashin aikin yi ke karuwa a kasar.

An dai gabatar da wannan shiri ne jim kadan bayan da gwamnatin ANC mai mulki ta ce ba za ta iya daukar nauyin biyan kudin karatun jami'a ba.